Thursday, August 31, 2023

Ango ya soke aurensu da amaryarsa bayan ya gano ta kaiwa tsohon saurayinta ziyarar bankwana

Manyan Labarai

Bankwana; A zamanin nan lamarin aure kan zo da tangarda sosai musamman duba ga yadda rashin gaskiya ya yawaita a tsakanin masoya wadanda ke son kulla auratayya a tsakaninsu.

Duk wata soyayya ko aure da aka gina bisa turbar karya, yaudara da cin amana baya kaiwa ko’ina domin da zaran wanda aka yiwa hakan ya gano toh sai a samu matsala.

Hakan ce ta kasance a bangaren wasu ma’aurata da ba a bayyana sunansu ba wadanda a yanzu sun shahara a shafukan soshiyal midiya bayan angon ya soke aurensu da amaryarsa a ranar daurin aure.

Angel FM’s Opanyin Darko wanda ya bayar da lamarin afkuwar lamarin daga Kasoa, kasar Ghana ya bayyana cewa mutumin ya gano cewar amaryar tasa ta ci amanarsa karo na karshe kafin aurensu.

An tattaro cewa wani abokin angon ne ya tsegunta masa lamarin da ya sa angon tayar da batun ana tsaka da liyafar bikinsu.

A wani bidiyo da ya yadu, an gano amaryar cikin hadadden doguwar rigar aurenta tana ihu tare da rokon mijin a kan ya yi mata rai amma fafur ya ki sauraronta.

Yadda jama’a suka dauki batun

Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin bayan an watsa bidiyon a kan soshiyal midiya.

Wasu na ganin barin batun da angon ya yi har sai da aka zo wajen shagalin bai kamata ba sam domin a cewarsu hakan tozarci ne kuma kamata yayi ace sun sulhunta a tsakaninsu ba wai kwance mata zani a bainar jama’a ba.

Wasu kuma sun ce lallai hakan na faruwa yadda yan mata kan ziyarci tsoffin masoyansu don yin sharholiyar karshe idan aka ce bikin aurensu ya gabato.

A nan mun tattaro maku wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

Irene Yeboah ta ce:

“Da ace ni ne shi da ba zan bata lokacina wajen samun wannan shaidanin ba faaa…kawai zan jira ka ne a wajen shagalin bikin don kwasar rawa.”

Albert Nana okyere ya yi martani:

“Wannan na iya zama gaskiya saboda na san wani da ya kwanta da budurwa kimanin mako daya kafin aurenta da ainahin saurayinta don haka zai iya faruwa.”

Frankjoe ya yi martani:

“Wai na rasa yadda wasu ke tunani? Aurenki sannan ki ziyarci wani tsohon saurayinki.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: