Thursday, May 30, 2024

Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Bayan Ya Gano Tana Da Yara Biyu Amma Ta Boye Masa

Manyan Labarai

Yan awanni kafin a daura masu aure, wani matashi ya ce ya fasa bayan ya gano cewa amaryar tana da yara biyu.

Bala Baba Dihis wanda ya wallafa mummunan labarin a Facebook ya ce abun ya faru ne da wani abokinsa.

A cewar Baba, an shirya daura auren ne a ranar Asabar, 17 ga watan Disamba.

Amaryar ta boyewa angon al’amarin amma sai ya gano da kansa.

Jama’a sun yi martani a kan al’amarin inda mutane da dama suka caccaki matar kan wannan babban kuskure da suka yi.

Martanin jama’a

AllaKaduna Nzeogwu ya ce:

“Ki ce wani abu.

“Bai kamata mutumin kirki kamarka ya riki siyasa da addini kawai ba a matsayin hanyar neman adalci da alkhairi a duniya.”

“Mugunta na zuwa ta hanyoyi daban-daban. Ka yi magana sannan ka tallafawa bawan Allah ya cimma kudirinsa…an gina shi a kan karya da yaudara. Za ka ceci al’umma.”

Sonia Dash ta ce:

“Zukatan wasu mutanen daga karfe aka yi shi.

“Ban zan taba fahimtar boye yara saboda kana son yin aure ba. Kuma wadannan abubuwan na ci gaba da faruwa.”

Arc Ehis Vheektor Onus ya ce:

Akwai matakai da dama da za a dauka a irin wannan yanayi… daya daga cikin matakan ggaggawa don hana afkuwar annoba a gaba shine wanda wannan gayen ya yi…Shin hakan na nufin dangin yarinyar gaba daya basu da tunani ne, cewa babu wanda zai iya bata shawarar yin abun da ya dace.”

Daniel Ogolo ya ce:

Matar ta so cin amana. Na so abun da ya yi. Ba batun haihuwar yara bane (ya dai rabu da ita) batun karfin halin boye irin wannan babban lamari ne daga gare shu. Irin wannan yarinyar zata iya ba mutum guba sannan ta yi ikirarin kuskure ne.”

Karamar yarinya ta ce mahaufinta take son aure

A wani labarin, wata karamar yarinya ta ba mutane mamaki a soshiyal midiya bayan ta kafe cewa mahaifinta take so da aure.

Yarinyar wacce ta saka doguwar riga irin na amare ta bukaci a fara daurin auren ba tare da bata lokaci ba lamarin da ya baiwa ma’abota bibiyar soshiyal midiya sha’awa da dariya sosai.

Duba nan: