Monday, August 28, 2023

A Watan Janairu Zan Sanar da Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zan Goyi Baya a 2023, Wike

Manyan Labarai

Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, yace nan da watan Janairun shekara mai kamawa zai bayyana wanda zai yi ma kamfen shugaban ƙasa a 2023.

Channels tv tace yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da gadar sama ta 10 da gwamnatinsa ta gina a ƙaramar hukumar Abio-Akpor, jihar Ribas, gwamna Wike yace jira ya ƙare.

Wike, jagoran tafiyar G5 a PDP wadanda suka ja daga da Atiku Abubakar, yace ba iya faɗin sunan ɗan takarar kaɗai zai yi ba, zai shiga yawo kwararo kwararo yana tallata manufofinsa a dukkanin jihohin Najeriya.

A kalamansa, Wike ya ce:

“Daga watan Janairu mai zuwa a shekara mai kamawa, zan faɗa wa mutane na wanda zasu jefa wa kuri’unsu.”

“Saboda haka baki dayanku da kuke ta sauraren matsayata, da waɗan da ke ta faɗin maganganu iri daban-daban a kaina, wasu na cin mutunci na da zagi, duk ku jira, watan Janairun ya kusa ƙarisowa.”

“Kar ku dauka fada maku wanda zaku zaba kaɗai zan yi, ko kadan zan ci gaba da yawo daga wannan jiha zuwa waccan ina yada manufarsa ina masa kamfe da kuma gaya wa mutane dalilin da yasa na ce su zabe shi, ba abinda zai faru.”

Tun watan Mayu PDP ta rasa zaman lafiya a cikin gida

News Brief Hausa ta gano cewa tun daga watan Mayu bayan kammala zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Wike ya shata layi tsakaninsa da Atiku.

Wike, wanda ya sha kaye a zaben, tare da wasu gwamnonin PDP huɗu da ake kira da tsagin gaskiya, sun kafe kai da fata dole sai shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

A cewarsu, babu adalci kwata-kwata dan takarar shugaban kasa dan arewa kuma shugaban jam’iyya ma dan arewa, bisa haka indai ana son daidaito dole ya ba dan kudu shugaban PDP na kasa.

A wani labarin kuma Jam’iyyar PDP Ta Dakatar da Kakaki A Jihar Gombe, Ya Yi Murabus

Har yanzu dai ana kai kawo game rikicin cikin gida a PDP a jihohin Najeriya da dama, a Gombe lamarin na neman faskara.

A ranar Alhamis ne aka ji Sakataren PDP na Gombe na cewa sun dakatar da mai magana da yawun jam’iyyar, Mustala Usman.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: