Wednesday, May 29, 2024

2023: Ku zabi mahaifina, yar Atiku ta roki matasa da daliban Najeriya

Manyan Labarai

Anambra – Maryam Abubakar, yar dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ta bukaci daliban Najeriya da matasa zu jefa wa mahaifinta kuri’a a zaben shugaban kasa da ke tafe.

Maryam ta yi magana ne a Awka a ranar Alhamis yayin wani taro mai lakabin “Anambra Youths/Students for Atiku” da dubban matasa da dalibai daga manyan makarantu da garuruwa suka halarta.

Atiku Abubakar da yarsa Maryam Abubakar
Atiku da yarsa Maryam Atiku. Hoto: Daily Nigerian

Ta bayyana mahaifinta a matsayin mutum wanda ya san darajar ilimi kuma zai bawa bangaren muhimmanci sosai don magance kallubalen da ake fama da shi.

Maryam Atiku: Mahaifina ya san darajar ilimi kuma zai magance kallubalen da ake fama da su a bangaren

Ta bukaci matasa su yi amfani da kuri’unsu don zaben mahaifinta a zaben da ke tafe, Daily Nigerian ta rahoto.

A cewarta:

“Ku yi imani da kanku, ku koyi darasi daga kurakurenku na baya kuma kada mayar da hankali kan abin da kuke yi. Ku yi imani da cewa da kuri’unku, za ku iya ceto kasar.

“Manyan saka hannun jarin da mahaifina ya yi a ilimi tsawon shekaru hujja ne da ke nuna ya yi imani da ilimi.”

Zaben 2023: Atiku masoyin matsa da ilimi ne – Ben Obi

A jawabinsa, Ben Obi, ciyaman din kamfen din Atiku/Okowa Organisation a jihar Anambra, ya bayyana Atiku a matsayin mai kaunar dalibai da matasa.

Ya ce Mr Atiku ya mayar da hankali don gina Najeriya ingantaciyya.

“A tare da Atiku za ka tarar da mutum da ya yi imani da ilimi. Bayan gina jami’a, Atiku yana bada tallafin karatu ga dalibai 250 duk shekara.

“Muna kira gare ku ku sake tattaro kan matasa da dalibai su zabi Atiku domin za ku amfana daga tsarinsa na sauya kasa.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: