Friday, September 1, 2023

2023: Atiku Da Tinubu Na Musayar Maganganu Kan Dukiya Da Mulki

Manyan Labarai

Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, PDP, Alhaji Atiku Abubakar da takwararsa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, counterpart, Asiwaju Bola Tinubu, suna ta musayar maganganu a yunkurin samun mulki ko ta halin kaka.

Yayin da kungiyar kamfen din shugaban kasa na Tinubu-Shettima , PCC, ta zargi dan takarar PDP da cewa yana da burin kwace mulki ta kowace hanya, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na Atiku, Mr. Phrank Shaibu, ya soki Tinubu kan ikirarin cewa ya gaji gidaje kuma ya siya hannun jari har ya yi arziki, Vanguard ta rahoto.

Labarin yadda Tinubu ya yi arziki shaci-fadi ne – Shaibu

Mr Shuaibu, mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai ga Atiku, ya soki ikirarin da Tinubu ya yi na cewa ya gaji arziki kuma ya siya hannun jari har ya yi kudi.

A cewarsa, Tinubu ya bada wannan tatsuniyan ne yayin amsa tambayar da aka masa kan tushen arzikinsa a hirar da ya yi da dan jarida na BBC a hirar da suka yi a baya-bayan nan.

Shaibu, a sanarwa ya ce:

“Bisa alamu Tinubu ya yi mamakin tambayar da dan jaridar BBC ya masa kan ya bayyana tushen arzikinsa mai ban mamaki, dan takarar shugaban kasar na APC ya amsa da cewa, ‘Kai makiyin arziki ne?’ Daga bisani ya bada tatsuniyar yada ya gaji kadarori kuma ya sayi hannun jari kamar Warren Buffet.

“Wannan shirme ne. Tabbas wannan shaci-fadi ne. Tinubu ya dena kwatantan asalin arzikinsa da Warren Buffet, wanda hukumomin Amurka ba su taba alakanta arzikinsa da miyagun kwayoyi ba.”

Tushen arzikin Tinubu

“Ba yau aka fara tambayar tushen arzikin Tinubu ba. Hukumomin Amurka sun bayyana cewa Tinubu ya yi aiki da Mobil Nigeria Limited a 1989 kuma albashinsa $2,400 kuma ba shi da wani hanyar samun kudi.

“Amma takardun Bankin First Heritage sun suna a 1990 (cikin shekara daya), Tinubu ya saka $661,000 cikin asusun bankinsa kuma a 1991 ya saka $1,216,500 a asusun. Ina ya samu kudin?”

Arzikin Atiku

“A bangare guda, tushen arzikin Atiku a bayyane ya ke. Wadanda ya lissafa sun hada da NICOTES (yanzu Intels) da aka kafa a 1989; Prodeco, 1996; Atiku Farms, 1982; da ABTI Schools, 1992.”

Da ya ke magana a wata kafar, dan takarar PDP Atiku Abubakar ya bayanansa a matsayin ma’aikacin gwamnati, dan kasuwa, cikin yan siyasa da suka yi gumurzu da sojoji don dawo da dimokradiyya sun saka shi gaban sauran yan takarar shugaban kasa na 2023.

Atiku ya bayyana hakan ne a jawabinsa a taron tattaunawa da yan takarar shugaban kasa a Channels Television a Abuja.

Ya ce:

“Najeriya bata taba shiga halin da ta shiga yanzu ba. Ina cikin wadanda suka yaki sojoji, na tafi gudun hijira. Ni da (abokin takara na) ta yiwu ba mu da dukkan amsoshi amma za mu gano hakan ta hanyar sauraron yan Najeriya, mun taho nan ne don sake sauraro.”

Zan yi amfani da kimiyya don magance matsalar tsaro

Atiku, wanda ya bayyana Boko Haram a matsayin abu mai daure hankali domin akwai abubuwa da yawa a cikin lamarin.

Ya yi bayanin cewa zai yi amfani da fasahar zamani da kimiyya don magance matsalar tsaro.

Ku yi taka-tsantsan da alkawuran Atiku – Tinubu

Da ya ke martani ga Atiku, Direktan watsa labarai na kwamitin kamfen din Tinubu-Shettima, PCC, Bayo Onanuga, ya ce ya kamata PDP ta zama cikin kunya saboda mulkin da ta yi daga 1999 zuwa 2015.

Cikin jawabinsa, Onanuga ya ce:

“Akwai bukatar mu gargadi yan Najeriya kan zakin baki da alkawurran tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da PDP a yayin da suka fara kamfen na ganin sun samu mulki ta kowanne hali.

“Tabbas wannan tarihi ne na karya. Ba za mu yarda a rude mu ba. Yan Najeriya ba su yarda da karyan da dan takarar shugaban kasar da jam’iyyar ke musu ba.”

Zan yi wa yan Najeriya adalci – Tinubu

A bangarensa, dan takarar shugaban kasa na APC, a jiya, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa zamansa shugaban kasa zai kawo karshen talauci, rashin tsaro da sauran matsalolin da ke addabar kasar.

Ya bayyana hakan ne a taron jin ra’ayin al’umma da ya yi da shugabannin musulmi daga yankin kudu maso yamma a Ibadan, jihar Oyo.

Tinubu ya samu rakiyar shugabannin kudu maso yamma karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Legas, Dr Femi Hamzat; dan takarar gwamnan APC a Oyo, Senata Teslim Folarin; Tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya, Dimeji Bankole; mataimakin direkta-janar na kamfen dinsa, Hadiza Usman da Sanata Fatai Buhari, da sauransu.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: