Wednesday, May 29, 2024

2023: Hakeem Baba-Ahmed Ya Fada Dalili 1 Da Zai Sa Ya Goyi Bayan Peter Obi

Manyan Labarai

Mai magana da yawun kungiyar dattawan arewa, NEF, Dr Hakeem Baba Ahmed, ya ce zai goyi bayan takarar Obi/Datti idan suna yan takara mafi cancanta a zaben shugaban kasa na 2023.

Dr Hakeem ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Hakeem Baba-Ahmed
Dr Hakeem Baba-Ahmed. Hoto: Daily

 

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed, kani ne ga Hakeem.

Ya ce:

“Kawai zan iya goyon bayan Obi da kanina Datti idan sune yan takara mafi cancanta. Ka san ina wani aiki tare da Kungiyar Dattawan Arewa, wanda zai bawa dukkan yan takara dama iri guda.”

Ya kara da cewa yan Najeriya da dama ba za su samu ikon yin zabe ba saboda rashin tsaro; ko INEC ba za ta iya yin zaben a yankunan ba ko mutanen ba za su iya fitowa su yi walwala ba.

Ya kuma ce:

“Akwai babban matsala da ya zama dole a magance ta. Idan ta dubi yankin kudu maso gabas, IPOB, yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, suna kai wa mutane hari suna hana su zirga-zirga.

“Ana hana mutane yin zabe domin wasu na kona ofisoshin hukumar INEC da kayayyakinsu.”

 

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: